http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/yadda-aka-yi-bikin-nada-sarki-charles-iii/7082204.html
Washington D.C. — Daruruwan dubban mutane ne suka yi jeru a titunan birnin London a ranar Asabar, don shaida bikin nadin sarautar Sarki Charles III, bikin da aka baje al’adu iri-iri da miliyoyin mutane suka kalla ta talbijin da kafar intanet a sssan duniya. Shugabannin kasashe, sarakun da sarauniyoyi 90 daga sassan duniya suka halarci bikin wanda aka yi a Westminster Abbey.