http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/gwamnatin-jihar-zanfara-ta-sassauta-dokar-hana-fita-albarkacin-ramadan/7019472.html
Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Magaji Dosar ya fitar a ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar ta ga ya dace ta daidaita lokacin dokar hana fita a fadin jihar da gwamnati ta sanya domin dakile yawaitar hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da satar kayan jama’a da barnata dukiyar gwamnati da na jama'a da sunan murnar samun nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka kammala a jihar. Sanarwar ta ce, "A yanzu dokar hana fitar ta koma daga...