http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/psg-na-gab-da-lashe-kofin-gasar-ligue-1/6540864.html
Lens na matsayi na bakwai ne a gasar ta Ligue 1, it ace kuma za ta kai wa PSG ziyarar. PSG na da maki 15 a saman teburin gasar, za kuma su lashe kofin ne a karo na 10 idan ba su sha kaye a hannun Lens ba. Kungiyar na da zaratan ‘yan wasa da suka hada da Lionel Messi, Kylian Mbappe da kuma Neymar, wadanda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito ya gansu suna atisaye a ranar Juma’ar nan.